Jul 12, 2022
Yadda 'Yan Siyasa Ke Raba Kan 'Yan Najeriya, Su Kuma Kansu A Hade
Najeriya kasa ce da Allah ya yi mata arziki, dimbin arziki sosai.
Wasu mashaharanta ma suna cewa, duk duniya ba wanda ya ke da arziki irin Najeriya.
Amma kuma ba talakawan da su ke wahala, kamar talawakawan Najeriya.
Talakawan kasar na biye wa siyasa da yan siyasa, su yi ta cece-kuce, da fada, da gaba, a wani lokacin ma har da kisan junansu a kan siyasa, a yayin da su kuma yan siyasar, manyansu da kananansu, ba haka suke yi ba, kullum su kansu a hade kuma maganarsu daya.
Shirin Najeriya a yau, ya duba matsalar, ok inda muka tattauna Dan siyasa, 'yan Najeriya da kuma masanin harkokin al'amuran yau da kullum.